Shin mai yasa zaka zabi Pierre-Emerick Aubameyang ?

Rahoto daga John Bennett na BBC World Service

Image caption Pierre-Emerick Aubameyang

Babu wani wasan farko da zai iya zarta wasan da Pierre-Emerick Aubameyang ya bugawa Borussia Dortmund a karo na farko a Bundesliga.

Dan wasan gaban na kasar Gabon ya ci Augsburg kwallaye uku a ranar farko ta kakar wasan inda nan take ya tabbatarwa da magoya baya cewa £11m da kungiyar ta biya domin kawo shi Jamus ba asara bace.

Da ma dai wannan shekara ce mai muhimmanci ga dan wasan mai shekaru 24.

A 2012 ya burge a gasar cin kofin Afrika a kasarsa daga bisani kuma ya ki amsa tayin Tottenham Hotspur.

Don haka a 2013 wajibi ne ga Aubameyang ya gwada cewa bajintar ta sa mai dorewa ce. Hakan kuma ya tabbatar.

Kwallon da ya ciwa St-Etienne a nasarar 3-0 da ta yi kan Bastia a watan Janairu ita ce ta bude kofar da ya yi ta cin kwallaye har bakwai a jere a wasannin gasar rukunin Ligue 1 na Faransa.

Aubameyang ya kammala gasar wasannin da kwallaye 19 kuma shi bayar aka ci a wasan karshe na cin kofin Faransa, lokacin da St-Etienne ta lashe babban kofinta na cikin gida na farko a sama da shekaru 30.

Manyan kungiyoyi da dama sun yi zabarinsa kuma dagewar da Borussia Dortmund, wacce ta doke Real Madrid ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai, ta yi domin tabbatar da ta dauke shi ya nuna irin muhimmancinsa.

Ba kowanne wasan kungiyar ta Jamus Aubameyang ke fara taka leda daga farko ba a yanzu amma kocinsa Jorgen Klopp ya ce: “tuni ya nuna cikakken tasiri” a daya daga cikin kungiyoyin da suka fi kwarewa a nahiyar Turai.

Tasirin har ya hada da mamakin da ya bai wa ‘yan kungiyar lokacin da suke samun horo inda yayi gudun mita 30 a kasa da lokacin da gwarzon tseren mita 100 na Olympics Usain Bolt ya yi.

Duk da kokarin Aubameyang, kungiyar kwallon kafa ta Gabon ta kasa rawar gani a 2013 amma dai a matakin kungiya, ko shakka babu wannan shekarar ta yi wa dan wasan gaban ya kyau.

Wannan ne kuma dalilin da ya sa yake da kuri’ata a gasar gwarzon kwallon kafa na nahiyar Afrika ta 2013.