Shin mai yasa zaka zabi Victor Moses?

Rahoto daga Nick Cavell na BBC Sports

Image caption Victor Moses na murza leda

Victor Moses ba irin ‘yan wasan nan ba ne da ke bukatar sai an take kwallo da shi a wasan kungiyarsa ko kasarsa kafin ya burge wurin taka leda.

Yana maraba da duk wata dama da ya samu, abinda ke tasiri wurin irin bajintar da yake nunawa duk san da ya shiga filin wasa.

Baya ga karfinsa da kwarewarsa, Moses dan wasa ne da zai iya buga kowacce lamba a gaba, abin da ke ba shi damar cin kwallo a muhimman lokuta.

A mafi yawan lokuta ana amfani da shi ne a matsayin dan wasan gefe amma a shirye yake ya rike matsayin mai kai hari na biyu duk san da bukatar hakan ta taso.

Wajibi ne Chelsea da Nigeria su godewa Moses bias gudunmawar da ya basu wurin lashe kofi a 2013.

A Chelsea, ya zura kwallo a wasanni bibiyun da aka yi a matakan daf da na kusa da na karshe da kuma na kusa da na karshe akan hanyarsu ta lashe gasar kofin Europa.

A gasar cin kofin kasashen Africa kuwa, ya na daga cikin ‘yan wasan da Nigeria ta dogara da su inda sau biyu yana cin bugun daga kai sai mai tsaron gida, wadanda suka taimakawa Super Eagles kai wa matsayin dab da na kusa da na karshe.

Shigar Moses cikin jerin wadanda za su iya lashe gasar gwarzon dan kwallon Africa shaida ce ta irin rawar da ya ke takawa a fage duk da cewa bai samu zuwa gasar cin Kofin Confederations tare da Nigeria ba a kasar Brazil a watan Yuni.

Hakika a tsawon shekarar nan ya sha fama da raunukan da suka hana shi halartar wasannin kasarsa da kuma kungiyarsa.

Duk da haka Moses ya zamo wani kusa a kungiyar Liverpool wacce ke nuna alamun farfadowa a farkon kakar wasanni ta 2013/2014 inda ya fara zurawa Swansea kwallo a wasan farkon day a buga jajayen.

Kasancewar Luis Suarez da Daniel Sturridge su ne zabin farko a matsayin ‘yan gaban Liverpool, babbar rawar da Moses zai taka a bana ita ce ta dan wasan gefe.