Ivory Coast ta kira Abdul Razak

Abdul Razak na Ivory Coast
Image caption Abdul Razak na Ivory Coast

An gayyaci tsohon dan wasan Manchester City Abdul Razak cikin tawagar Ivory Coast da zata kara da Senegal a zagaye na biyu na wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

An kira dan wasan mai shekaru 20 da ke bugawa kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha ne tare da Ismael Diomande na kungiyar Saint-Etienne ta Faransa.

'Yan wasan biyu zasu maye gurbin Cheick Tiote na Newcastle ne da Geoffroy Serey Die na Basel, wadanda aka dakatar da su.

An dai basu jan kati ne a karawar farko tsakanin kasashen biyu da aka yi a Abidjan, inda Ivory Coast ta yi nasara 3-1.

Za'a buga wasa na biyun ne ranar 16 ga Nuwamba a Casablanca saboda haramtawa Senegal wasa a gidanta da aka yi.

Kungiyar da ta yi nasara tsakanin kasashen biyu za ta samu zuwa gasar cin kofin duniya da za'a yi a Brazil 2014.