Tottenham ta casa Sheriff Tiraspol 2-1

Jermain Defoe ya kafa tarihi a Tottenham
Image caption Jermain Defoe ya kafa tarihi a Tottenham

Jermain Defoe ya zama dan wasan Tottenham na farko da yaci kwallo 23 a Turai a wasan da suka samu nasara kan Sheriff Tiraspol tare da samun gurbi a matakin sili biyu kwale na gasar Europa.

Dan wasan gaban na Ingila ya ci da fenariti ne bayanda Erik Lamela ya ciwa kungiyar kwallon farko a wasan.

Kwallon da Ismail Isa ya farke ita ce ta farko da aka zura a ragar Tottenham a gasar Turai a kakar bana.

Kungiyar za ta iya hayewa saman teburin rukuninta ko da canjaras ta buga a wasan da za su sake nan da makonni uku a Tromso.