United ta doke Arsenal 1-0

Robin Van Persie
Image caption United ta koma matsayi na biyar a teburin Premier

Manchester United ta dan takawa Arsenal burki a kokarin da take na ganin ta lashe kofin Premier bana, bayan da tsohon dan kwallon Arsenal Robin Van Persie ya zura mata kwallo.

United ta zura kwallo a raga a minti na 27 lokacin da Rooney ya kwaso kwana Robin Van Persie ya yi tsalle ya zura kwallo da ka.

Arsenal ita ce tafi taka kwallo a karawar, har ma ta sami dama ta hannun Oliver Giroud da ya buga kwallo ta kaucewa raga da yadi biyu.

Wannan sakamakon yasa United ta koma matsayi na biyar a teburin Premier, Arsenal kuma ta baiwa United tazarar maki biyar.