"Sai mun gyara wasaninmu na waje"

Manuel Pellegrini
Image caption Kocin ya damu da rashin nasara a wasannin waje

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce: "Sai mun gyara salon wasannin mu na waje idan har muna son lashe kofin Premier ta bana."

City ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Sunderland ranar Lahadi, sannan ta fado matsayi na takwas a teburin Premier, kuma kungiyar ta sami maki hudu kacal a maimakon maki 18 da ya kamata ta samu a wasannin waje.

Pellegrini ya ce "Na damu matuka yadda muke barar da maki a wasanninmu na waje, kuma yana da mutukar wahala ka lashe kofin Premier idan baka lashe wasannin waje"

City ta lashe dukkan wasanninta na gida guda biyar a kakar wasan bana, ta kuma yi rashin nasara a wasannin da ta buga a waje da kungiyoyin Cardiff da Aston Villa da Chelsea da Sunderland.