Fargaba ce ta cuce mu - Wenger

Arsene Wenger
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce fargaba ce ta hana 'yan wasansa nasara a kan babbar abokiyar adawarsu Manchester United.

Kwallon da Robin van Persie ya jefa da ka, kafin tafiya hutun rabin lokaci ce ta bai wa United nasara. Rabon Arsenal da lashe wasa a Old Trafford dai tun shekarar 2006.

"Muna cikin dar-dar ne a kashin farko na wasan," in ji Wenger.

Faduwar Arsenal a Premier a karo na farko cikin wasanni shida na nufin ta na nan a saman tebur da maki 25, inda Liverpool ke biyo bayanta da tazarar maki biyu, ita kuma United ta koma ta biyar da maki 20.