Kebede zai buga wasan Ethiopia da Nigeria

Nigeria ce ta yi nasara 2-1 a karonta na farko da Ethiopia
Image caption Nigeria ce ta yi nasara 2-1 a karonta na farko da Ethiopia.

Dan wasan gaba Getaneh Kebede zai taka wa Ethiopia leda a wasansu da Nigeria a karonsu na biyu na wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za'a yi ranar Asabar a Calabar.

Dan wasan na Bidvest Wits mai shekaru 21 bai buga wasan farko, wanda Nigeria ta yi nasara 2-1 ba saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.

Kocin Ethiopia Sewinet Bishaw zai yi farin cikin dawowar dan wasan mai yawon cin kwallo daidai lokacin da kungiyar ke kokarin kai wa ga gasar cin kofin duniya da za'a gudanar a Brazil 2014.

Dan wasan gaba Saladin Seid da na tsakiya Shimels Bekele na cikin 'yan wasan da za su fafata a karawar.

Ranar Litinin Kebede ya yi atisaye da sauran 'yan kungiyar wadanda mafi yawansu a gida suke buga wasa.