Ba zamu bar 'yan kwaya a Olympics ba

Thomas Bach
Image caption Shugaban Olympics na Duniya

Shugaban Kwamitin Olympic na Duniya Thomas Bach ya sanarwa da BBC ce wa hukumar sa ta shirya domin dakatar da duk wata kasa da ba ta da ingantaccen tsarin gwada 'yan wasa masu amfani da abubuwan kara kuzari.

Back ya ce duk wata kasa da hukumar kula da ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari ta ambato a jerin marassa kyakkyawan tsarin, zamu dakatar da ita nan take.

Ba mu taba dakatar da wata kasa da ta gaza wajen gwajin amfani da abubuwa masu kara kuzari ba a gasar Olympic. Sai dai wakilin BBC ya ce ana shirin bai wa hukumar kula da shan kwayoyi masu kara kuzari ta duniya wuka da nama nan da dan lokaci mai zuwa.

Bach da ke halartar taro a Johannesburg kan shan kwayoyi a lokacin wasanni, ya ki amsa tambaya akan Jamaica ko za a dauki mataki a kanta, tunda an sami 'yan wasanta da dama masu shan kwayoyin kara kuzari.