Ba ji don ba'a kira ni Super Eagles ba - Uche

Magoya bayan Super Eagles ta Nigeria
Image caption Magoya bayan Super Eagles ta Nigeria.

Dan wasan Villareal mai tashe Ikechukwu Uche ya ce bai damu da rashin gayyatarsa ya bugawa Nigeria kwallo ba.

Duk da cin kwallaye uku cikin wasanninsa hudu na baya bayan nan a Spain, kocin Nigeria Stephen Keshi bai gaiyace shi cikin kungiyar Super Eagles ba.

Sai dai ya shaidawa BBC; "Har abada ina goyon bayan Super Eagles kuma idan an gaiyace ni zan je."

Nigeria ta nan jan Ethiopia da ci 2-1 kuma za su buga wasansu na biyu na neman shiga gasar kofin duniya a Calabar.