Zamu casa Nigeria in ji kocin Ethiopia

Etiopia vs Nigeria
Image caption 'yan kwallon Ethiopia da suke murnar zura kwallo

Kocin Ethiopia Sewnet Bishaw, ya ce za suyi iya kokari suga sun doke Nigeria a wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin duniya da zasu fafata ranar Asabar.

Ethiopia na fatan kaiwa wasan kofin duniya lokacin da za su kara da Nigeria, duk da rashin nasarar da su kayi a karawar farko da ci 2-1 a birnin Addis Ababa.

Bishaw ya shaidawa BBC ce wa "wannan shine gagarumin wasan da nake son lashe a rayuwata, ina matukar son lashe wasan, sai inda karfi na ya kare."

Ya kara da ce wa "bani da wata matsala da 'yan wasa na, dukkansu suna cikin kocin lafiya, kuma suna dokin lashe Nigeriya.

Nigeriya ta lashe karawar farko da su kayi a Addis Ababa kuma Emmanuel Emenike ne ya zura kwallayen biyu, kuma tuni ake tunanin Nigeria tafi samun dama da kuma fatan kaiwa gasar kofin duniya karo na biyar.