Ivory Coast za ta gasar cin Kofin duniya

'Yan wasan Ivory Coast
Image caption Ivory Coast za ta Kasar Brazil a 2014

'Yan wasan Kasar Ivory Coast sun sami nasarar tsallakewa zuwa gasar kofin duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Kasar Ivory Coast din ta samu nasara ne a karawarsu ta biyu da Senegal da ci 1-1.

A karawar farko Ivory Coast a gida ta ci Senegal din 3-1.

Yanzu sakamakon ya kasance Ivory Coast ta yi galaba da ci 4-2.

Kungiyoyin kwallon kafa guda uku nan gaba za su hade da Kasashen Najeriya da Ivory Coast domin su cike gurbin Kasashen Afirka biyar zuwa gasar cin Kofin duniyar.