Nigeria za ta sada zumunci da Italiya

Image caption Super Eagles na atisayen zuwa Brazil 2014

Da yammacin Litinin ne Nigeria za ta buga wasan sada zumunci da Italiya a filin wasa na Craven Cottage da ke London.

Wasan da kungiyar da ta daga kofin duniya sau hudu na zuwa kwanaki biyu bayan da Nigeria ta zamo kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta samu shiga gasar cin kofin ta Brazil 2014.

Nigeria dai ta yi nasara kan Ethiopia ne 4-1 a wasanni biyun da suka buga.

Wasan da za'a take da karfe 7:45, shi ne wasan sada zumunci da wata kasar Turai na farko da Super Eagles za ta buga tun bayan da Stephen Keshi ya zama kocinta a 2011.