Nigeria za ta lashe Brazil 2014 - Enyeama

Vincent Enyeama
Image caption Vincent Enyeama na sa ran Nigeria za ta zamo kasar Afrika da za ta lashe gasar cin kofin duniya a karo na farko.

Kyaftin din kwallon kafar Nigeria Vincent Enyeama ya ce ya yi imanin kasar za ta iya lashe gasar kofin duniya da za'a yi badi a Brazil.

Super Eagles ce kungiyar Afrika ta farko da ta samu tikitin shiga gasar bayan ta doke Ethiopia 4-1 a wasanni biyu.

Sai dai wannan yakini na Enyeama ya sabawa tarihi da kuma yanayin wasan Nigeria na baya bayan nan.

Rabon Nigeria da cin wasa a gasar duniya tun nasarar da ta samu a kan Bulgaria a 1998 kuma ita ce karo na karshe da Super Eagles ta fito daga rukuninta.

A tarihin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, kasashen Afrika uku ne kacal suka taba kai wa matakin daf da na kusa da na karshe: Cameroon a 1990, Senegal a 1992 da Ghana a 2010.