An shawarci Haye ya daina Dambe

David Haye
Image caption ''Ina da babban buri a shekara mai zuwa kuma shi ne na sake ciyo kambin duniya'', inji Haye

An shawarci tsohon zakaran damben boksin na duniya David Haye na Birtaniya da ya yi ritaya daga wasan.

Likitoci ne suka ba shi shawarar bayan da aka yi masa aiki tsawon sa'a biyar a kafadarsa ta dama a Jamus.

Dan damben mai shekaru 33 ya ce wannan mummunan labari ne a gare shi, saboda ba haka ya so ya kare shekara ta 2013 ba.

A watan Oktoba na 2011 Haye ya sanar da ritayarsa daga damben boksin.

Bayan Wladimir Klitscho na Ukrain ya casa shi ya karbe kambinsa na WBA a Jamus,amma ya dawo fagen bayan shekara daya.