Eagles sun fara hutun karshen shekara

Image caption Keshi ya gargadi 'yan Super Eagles su zage dantse

'Yan kwallon Najeriya Super Eagles sun tafi hutun shekara bayan wasan sada zumunta da suka buga da Italiya 2-2 a Ingila.

Kociyan kungiyar kwallon kafar ta Super Eagles Stephen Keshi wanda ya yiwa 'yan wasan jawabi cewa sun yi kokari, amma ya ce kamata yayi su kare wasan wannan shekarar da nasara kan Italiya.

Keshi ya yi musu fatan alheri a hutun Kirsimati da kuma sabuwar shekara kafin lokacin ya zo.

Kocin ya kuma umarce su da su zage dantse a kulob-kulob dinsu domin a cewar sa ba kowa ne zai iya dawo wa ya bugawa kasar gasar cin kofin duniya ba.

Ya ce su kara kaimi wajan fitowa a wasanni da kuma azama wajan nuna bajin tarsu kafin lokacin da za a kirawo wadanda suka cancanta.

Karin bayani