Enrique zai yi jinyar wata daya

Image caption Lius Enrique

Kocin Liverpool Brendan Rodgers, ya ce dan wasansa Jose Enrique ba zai buga wasansu da Everton a ranar Asabar ba, saboda rauni a gwiwarsa.

Enrique dan Spain mai shekaru 27 zai yi jinyar wata guda.

Rodgers ya ce raunin dan kwallon ba zai yi wa kulob din dadi ba.

Enrique ya koma Anfield daga Newcastle a kan fan miliyon shida a watan Agustan 2011.

Liverpool ce ta biyu a kan jadawalin gasar a yayinda za ta kara da makwabciyar ta Everton a filin Goodison Park.

Karin bayani