Ibrahimovic ba zai kalli gasar 2014 ba

Image caption Ibrahimovic ya damu da rashin fitowarsu gasar 2014

Kyaftin din kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic ya ce ba zai kalli wasan gasar cin kofin duniya ba bayan da kasar Portugal ta lallasa su.

Wasan dai shine ya sa Sweden din ba ta iya fita gasar cin kofin kwallon kafa na duniyar ba da za a yi a Brazil 2014.

Ibrahimovic mai shekaru 32 ya ce, " abin da na tabbatar shine kwallon kafa na duniya babu ni ai abune da ba zan bibiye shi ba.

Wasan Sweden da Portugal tamkar wani gware ne tsakanin Ibrahimovic da kuma Cristiano Ronaldo wadanda duka gogaggun 'yan wasa ne a duniya.