Hodgson bai kadu da cinsu biyu a gida ba

Image caption Cin Ingila sau biyu a Wenbley bai kada Hodgson ba

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya takarkare cewa nasara da aka samu kan Ingila a filin wasa na Wembley sau biyu ajere wanda ba a taba yin irinta ba tun 1977 ba abu ne da za a dimauce akai ba.

Chile ce dai ta fara cin Ingila 2-0 ranar Juma'a a wasan sada zumunta sannan kuma Jamus ta ci Ingilar ranar Talata.

Roy Hodgson ya ce " ba wani abu ne da za a wani dimauce ba".

Ya kuma ce shekara ce mai girma a gare shi duk kuwa da nasarar da akayi akansu guda biyu a jere.

Karin bayani