Fabrice Muamba zai koma aikin jarida

Image caption Fabrice Muamba ya hakura da wasan kwallon kafa

Dan wasan nan Fabrice Muamba wanda ya fadi a wasan dab da na karshe na Premier League a watan Maris 2012 ya murmure, amma zai koma aikin jarida.

Dan wasan wanda zuciyar sa ta tsaya da bugawa ya fuskanci rayuwarsa ta gaba inda ya zabi ya koma dan jarida mai kawo rahotannin wasanni.

Muamba ya ce, " na dai karanta a jaridu abin da ya faru da ni amma ban taba kallon lamarin ba da ya faru a filin wasan White Hart Lane ba."

Muamba yana kuma koyon aikin jarida na wasanni.

Sai dai yana yiwa 'yan jarida barkwanci, ya kyalkyale da dariya; ya ce " ba kwace muku aiki zan yi ba".

Karin bayani