Joe Hart zai dawo wasa

Joe Hart
Image caption Hart ya sha suka a kan kurakuren da ya yi musamman a wasan City da Bayern Munich a watan da ya wuce

Joe Hart zai dawo tsaron raga a wasan da Manchester City za ta yi da Viktoria Plzen na Zakarun Turai ranar Laraba.

Kociyan Manchester City Manuel Pellegrini ne ya sanar da shirin dawo da mai tsaron gidan na Ingila wasa.

Rabon da Hart yayi wasa tun lokacin da Costel Pantilimon ya maye gurbinsa a wasan City da Norwich na Premier ranar 2 ga watan Nuwamba.

Maitsaron gidan dan shekara 26 bai buga wasan Ingila da Chile ba amma kuma yayi rawar gani a wasan kasar da Jamus a makon da ya wuce.

Pellegrini ya ajiye Hart bayan da Chelsea ta ci su 2-1 a Stamford Bridge a karshen watan da ya gabata.

Bayan da Hart da dan wasansu na baya Matija Nastasic suka yi kuskure har Torres ya ci su a dai-dai lokacin tashi.

Pellegrini ya ce ajiye Hart abu ne mai wuyar gaske amma kuma maitsaron gidan yana bukatar hutu.

Karin bayani