Mun ji kunya in ji Villas-Boas

Andre Villas-Boas
Image caption Villas-Boas ya ce, ''a yanzu burina shi ne na karawa 'yan wasan kwarin gwiwa a wasanninmu da ke tafe.''

Kocin Tottenham ya ce tawagarsa ta ji kunya saboda kashin da ta sha a wajen Manchester City daci 6-0.

Dakikoki 14 da fara wasa kacal aka zura wa Spurs kwallon farko, kuma wasan shi ne rashin nasara mafi muni da kungiyar ta fuskanta tun bayan da Newcastle ta doke ta da ci 7-1 a 1996.

A yanzu Tottenham ta koma ta tara a tebur, kuma Arsenal ta dara ta da maki takwas.

Ke nan Tottenham ta samu maki daya cikin wasanni uku a jere.