Baines ya karya dan yatsa

Image caption Leighton Baines

Dan kwallon Everton Leighton Baines, zai yi jinyar kwanaki 10 zuwa makwanni shida bayan da ya karya dan yatsa a karawarsu da Liverpool a ranar Asabar.

Dan kwallon mai shekaru 28 an sauya shi bayan minti 50 da soma wasan inda aka tashi 3 da 3 a Goodison Park.

Kocin Everton Roberto Martinez ya ce "Leighton ya samu karaya a yatsarsa ta kafar dama."

"A don haka ba zai taka leda ba na makwanni shida, amma ya danganta da warkewar kafar da wuri."

Karin bayani