Blatter ya soki Betis kan nuna wariya

Sepp Blatter
Image caption Blatter ya ce sai an dauki kwararan matakai, ba wai cin tara ko dakatar wa ba

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya yi kakkausar suka ga magoya bayan Real Betis, bayan da suka yi wa dan wasan kungiyar Paulao kalamun wariya.

Magoya bayan kungiyar sun yi ta yin kalamun wariya ga mai tsaron bayan kungiyar Paulao, lokacin da aka ba shi jan kati a karawar da suka yi da Sevilla suka kuma sha kashi da ci 4-0.

Sai dai alkalin wasa bai rubuta faruwar haka ba a rahotansa na bayan kammala wasa.

Blatter ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewa "abin takaici kungiya ta yi wa dan wasanta kalamun wariya, a inda ya yi Allah-wadai da halayyar da miliyoyin mutane suka gani a akwatin telebishin da yanar-gizo.

Ya kara da ce wa "ba sani ba sabo idan za a yaki kauda kalaman wariya, abin ya fi karfin cin tara, sai da daukar hukunci mai tsauri".

Ita ma kungiyar ta rubuta a shafinta na Tweeter ce wa ba ta amince da dukkan wani tashin hankali ko kalaman wariya ga dan wasan kungiya ko abokan karawa ba.