Bana tsoron a kore ni - Keshi

Stephen Keshi
Image caption Kocin ya ce baya bukatar mai koyarwa daga Turai

Kocin Nigeria Stephen Keshi, ya ce baya cikin damuwa ko kasar za ta kore shi daga aikinsa kafin buga gasar cin kofin duniya a Brazil a shekara ta 2014.

Keshi ya jagoranci Nigeria shiga gasar cin kofin duniya a badi, bayan da ya lashe Ethiopia da ci 4-1 a wasan cike gurbi da suka kara gida da waje.

Kocin ya taba samun irin wannan damar har karo biyu, daga baya aka sallame shi.

A shekara ta 2002, Keshi ya yi wa Shuaibu Amodu mataimaki lokacin da Nigeria ta samu gurbin shiga kofin duniya,amma aka koresu aka maye gurbinsu da Adegboye Onigbinde kafin halartar gasar kofin duniya a Koriya ta Kudu da Japan.

Bayan shekaru hudu, Keshi ya sama wa Togo gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Jamus ta karbi bakunci a shekara ta 2006, karon farko da kasar ta samu gurbi shiga kofin duniya, dfa har yanzu bata sake samu ba.

Kocin ya shaidawa BBC ce wa "dama aikin ya gaji a dauke ka, a kuma sallameka, nayi matukar mamakin lokacin da aka sallameni a shekarar 2002, amma baza ka bari bacin rai ya dame ka ba, sai kaci gaba da rayuwa.