Fifa ta jaddada hukunci akan Ukraine

San Marino Ukraine
Image caption Blatter ya ce dole a dauki tsauraran matakai akan kalamun wariyar launin fata

Fifa ta ki amincewa da daukaka kara da Ukraine ta shigar bisa hukuncin da aka yanke mata na buga wasa babu 'yan kwallo a wasan farko da za ta yi a gida a neman zuwa gasar kofin duniya ta shekarar 2018.

An ladabtar da Ukraine din ne bayan da aka samu magoya bayan kasar da kalaman wariyar launin fata lokacin da suka kara da San Marino a wasan neman shiga gasar kofin duniya ta shekara ta 2014.

Haka kuma Fifa ta ci tarar kasar akan wannan laifin da ta nuna a filin wasanta.