Cikin 'yan wasan Man United ya kadu

Moyes da Rooney
Image caption David Moyes na farin ciki Wayne Rooney na wasansa da zuciya sosai yanzu

Wasu 'yan wasan Manchester United sun kadu bayan da jirgin da ya kai su Jamus domin wasansu da Bayern Leverkusen na Zakarun Turai na Larabar nan ya fasa sauka.

Jirgin ya fasa sauka ne a filin jirgin sama na Cologne/Bonn na Jamus gab da lokacin da zai sauka, mita 400 tsakaninsa da kasa.

Sai dai daga baya a karo na biyu jirgin ya sauka lami lafiya, amma kuma jami'an kungiyar ta Man United sun ki cewa komai game da lamarin.

Rio Ferdinand ne kawai yayi ta maza ya dan yi magana ya ce, '' mun sauka a Jamus.....yanzu.....yanzun nan na farfado daga wannan fargaba ta saukar jirgin! ''

Daman a shekarar 1958 'yan wasan kungiyar ta Man United sun yi hadarin jirgin sama a birnin Munich na Jamus inda mutane 23 suka mutu a cikinsu.

Kungiyar ta Manchester United za ta tsallake zuwa zagayen 'yan 16 na sili biyu kwale idan tayi nasara a karawar da za su yi yau.

Kociyan United David Moyes ya dogara ga Wayne Rooney ya kai su zuwa matakin na gaba saboda Robin van Persie yana jiyya.

Karin bayani