Ya dace da aka lashe mu — Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Kocin ya ce basu taka rawar gani ba a Basel

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya ce abin tunkaho ne a gare su da suka kai matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun Turai duk da cewa Basel ta doke su da ci daya mai ban hausi.

Dan kwallon Basel Mohamed Salah shi ne ya zura kwallo daf a tashi wasa, bayan da aka canja Samuel Eto'o sakamakon raunin da ya ji.

Sai dai Chelsea ta samu kai wa matakin gaba, bayan da Schalke da Steaua Bucharest suka tashi babu ci a wasansu.

Mourinyo ya ce "ba mu taka rawar gani ba, ya kuma dace da muka yi rashin nasara, kuma sai sakamakon wani wasanne ya ba mu damar kai wa zagayen gaba."

"Babu wani abu da ya burge ni a wasanmu, masu tsaron bayanmu sun yi kura kurai da dama."