Fifa ta amince da wasan Afrika ta kudu da Spain

South Africa Team
Image caption Fifa ba za ta dauki mataki akan Afrika ta kudu ba

Afrika ta kudu za ta ci gaba da rike makin da Fifa take bayarwa na jerin kasashen da suka fi iya taka kwallo a duniya, bayan da hukumar ta sanar da cewa lashe Spain da kasar tayi ranar 19 ga wata babban wasa ne.

Tun a farko Fifa tayi kokwanton ingancin wasan sada zumunci da su ka kara, saboda Spain ta sauya 'yan wasa bakwai a fili.

Fifa ta ce "ba za ta dauki wani mataki akan afrika ta kudu ba, domin tabi ka'idojin wasa, a inda ta canja 'yan wasa shida."

Sai dai hukumar ta ce za ta iya daukar mataki akan Spain mai rike da kofin duniya.