Ina son in ci gaba da haskakawa - Bale

Image caption Bale da Ronaldo na murnar lallasa abokan hammaya

Gareth Bale na son ya ci gaba da zura kwallaye a kungiyarsa, a yayinda Real Madrid za ta dauki bakuncin Real Valladolid a ranar Asabar.

Dan kwallon Wales din mai shekaru 24, ya zura kwallaye biyar a wasanni shida a jere da ya bugawa kulob din.

Bale yace" Ina jin dadin murza leda kuma ina fatan in ci gaba da haskakawa."

Kocin Real Carlo Ancelotti kawo yanzu bai bayyana tsawon lokacin da Cristiano Ronaldo zai shafe yana jinya ba.

Bale ya koma Real daga Tottenham a kan fan mliyan 85.

A yanzu haka dai Real Madrid ce ta uku a kan teburin gasar La Liga, inda Barcelona ke ta farko sai Athletico ke ta biyu.

Karin bayani