Wilfried Bony zai yi jinyar makwanni

Image caption Wilfried Bony

Kocin Swansea Michael Laudrup, ya ce dan wasansa Wilfried Bony zai yi jinyar makwanni, saboda rauni matse-matsinsa.

Bony mai shekaru 24, ya ji raunin ne a wasan da suka sha kashi a hannun Valencia daci daya me ban haushi a gasar Europa.

Laudrup ya ce "Raunin na da tsanani kuma zamu jira sakamakon gwaje-gwajen da za a yi masa."

Dan kwallon Ivory Coast din ya ci wa Swansea kwallaye 10 a kakar wasa ta bana.

Haka zalika daya dan kwallon Swansea na gaba, Michu har yanzu bai murmure ba.

Karin bayani