''Zan dawo da Sir Alex Tottenham''

Sir Alex Ferguson
Image caption Sir Alex ya bar aikin kociyan Man United bayan shekaru 27 ya zama darekta a kungiyar

Tsohon shugaban kungiyar Tottenham Lord Alan Sugar ya ce zai yi kokarin shawokan Sir Alex Ferguson ya dawo aikin kociya a Tottenham.

Lord Sugar ya ce, ''fatana shi ne babban abokina Sir Alex Ferguson zai ji sha'awar dawo wa fagen wasa.

Nan da shekara daya ya dawo da kyakkyawar matarsa London ya koyar da kungiyarmu.''

''wannan shi ne fata ne. Idan ya zo kallon wasa, zan bashi shawarar gidaje masu kyau da shi da matarsa za su zauna.''

A cikin kwanakin nan ana rade radi kan ci gaba da zaman Andre Villas-Boas a kungiyar Tottenham.

Sakamakon lallasa kungiyar da Manchester City ta yi da ci 6-0 ranar Lahadi.

Villas-Boas ya maida martani akan maganar tsohon shugaban kungiyar inda ya nuna bai damu ba.

Ya ce, ''ai da tarihin da Sir Alex ya kafa ya isa ya yi wa duk wata kungiya kyakkyawan kociya.''

Karin bayani