Giggs ba shi da niyyar ritaya

Ryan Giggs
Image caption Giggs ya zarta Gary Neville da Paul Scholes da suma suka yi wasansu gaba daya a Man United

Ryan Giggs na Man United ba shi da niyyar dena wasa duk da cewa ya cika shekara 40 da haihuwa ranar Juma'an nan.

Gigggs dan yankin Wales duk tsawon rayuwarsa ta kwallon kafa yayi ta ne a Old Trafford inda yayi wa kungiyar wasanni 953, tun bayan da ya fara mata wasa da Everton a 1991.

Ya ce,'' abu ne da zai iya kasancewa mai wuya wasu lokutan amma har yanzu ina jin dadin buga wasa.In dai haka za ta kasance to zan ci gaba da yi.''

Ya ce, '' na yi sa'a da na kasance a kungiya daya, inda nake tare da 'yan wasa da kociya masu kyau.''

Dan wasan ya kara da cewa, da ya rika sauya kungiya to da yanzu ya dena wasa (ta kare masa) kamar sauran takwarorinsa na 1992.

Kamar su David Beckham da Phil Neville da Nicky Butt.

A karshen kakar wasannin nan kwantiraginsa zai kare, kuma idan aka kara masa shekara daya zai kasance shekara 24 a kungiyar, da yi mata wasanni 1,0000.

Karin bayani