An fara saida tikitin gasar kofin Afrika

South Africa Stadium
Image caption Filin wasan da za a bude gasar cin kofin Nahiyar Africa ta 'yan kwallon dake wasa a Afrika

An fara sayar da tikitin shiga kallon gasar cin kofin nahiyar Afrika da Afrika ta kudu za ta karbi bakunci.

Gasar da aka shirya don 'yan kwallon dake buga wasa a Afrika, kuma karo na uku da za a gudanar da gasar ranar 11 ga watan Janairu.

Tuni aka samu kasashe 15 da kuma mai masaukin baki Afrika ta kudu da kuma Jamhuriyar Congo da ta lashe gasar karon farko.

Tuni aka yi waje da mai rike da kofin karo na biyu Tunisia, wanda Morocco ta maye gurbinta.

Ga yadda aka raba rukunnan kasashen

Rukunin farko: South Africa da Mali da Nigeria da Mozambique Rukuni na biyu: Zimbabwe da Uganda da Burkina Faso da Morocco Rukuni na uku: Ghana da Libya da Ethiopia da Congo Rukuni na hudu: Gabon da Burundi da Mauritania da Jamhuriyar Congo