'Yan wasa za a zarga ba koci ba - Parker

Kaftin din Fulham Scott Parker ya ce bai kamata a dinga ganin laifin koci Martin Jol a kan rashin kokarinsu a gasar Premier ba.

Jol yana shan suka bayan da suka yi rashin nasara a hannun West Ham, kuma rashin nasarar wasanni biyar a jere da suka kara kenan.

Parker ya shedawa BBC ce wa "Kodayaushe mai horarwa kan dauki laifin rashin kwazo, amma 'yan wasa ya kamata a baiwa babban laifi."

Image caption Kocin yana fuskantar kalu bale a kungiyar Fulham

Fulham ba ta kai hari ko sau daya ba a ragar West Ham da aka lashe su da ci 3-0, sai dai Parker ya ce suna iya kokari suga sun saka kaima a wasa kada a kori mai horar da kungiyar.