Ina murna da wasannina — Robben

Arjen Robben
Image caption Robben zai ci gaba da kwazo a kakar bana

Dan kwallon Bayern Munich Arjen Robben ya ce ya yi murna bayan da ya zura kwallaye biyu a wasan da suka lashe Eintracht Braunschweig da ci 2-0 a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekaru 29 ya zura kwallo na 50 da kuma ta 51 a wasanni 90 da ya buga Bundesliga, a lissafance ya zura kwallo a duk bayan minti 125.

Robben ya zura kwallaye hudu a wasanni uku da ya bugawa Bayern Munich, bayan da ya yi wasanni uku a baya bai jefa kwallo a raga ba.

Dan wasan dan kasar Holland, ya koma Bayern daga Real Madrid a shekarar 2009, ya zura kwallaye 17 ya kuma taimaka aka jefa kwallaye har sau 11 a wasanni 26 da ya buga wa zakarun kofin Turai a baya.