Ruud Krol ya raba gari da CS Sfaxien

Ruud Krol
Image caption Kocin ya ce sun dade suna fama da rashin kudi a kungiyar

Rudd Krol ya bar kocin kungiyar kwallon kafa ta CS Sfaxien, saboda rashin biyan hakkokinsa da sauran matsalolin kudi a kungiyar.

Kocin mai shekaru 64, tsohon kaftin din Holland ya bar kungiyar ne kwana guda, bayan da kungiyar ta lashe kofin zakarun Afrika wato Confederation Cup a wasan da suka zura kwallaye 3-2 akan TP Mazembe.

Krol ya bar kungiyar ne bayan shekara guda da yayi, a inda kungiyar ta lashe kofin Tunisia a watan Mayu, rabonta da kofin tun shekaru takwas.

Kocin ya sanarwa da BBC ce wa "kungiyar tana fama da matsalolin kudi, wanda ni da 'yan wasa mukan ji jiki tun tsawon lokaci da dama."