Kocin Ingila ya fi damuwa da filin wasa

Roy Hodgson
Image caption Kocin ya na fata Ingila za ta taka rawar gani a Brazil

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce ya fi mai da hankali kan filin da za su kara a gasar cin kofin duniya akan kasar da za su hadu a cikin rukuni.

Hodson zai san kasashen da Ingila za ta hadu da su a rukuni da filaye da kuma lokutan da za su kara a gasar cin kofin duniya a ranar Juma'a a Salvador da ke Brazil.

Ingila wacce ake ganin ba ta kan gaba-gaba a jerin kasahen da suke jagaba a kwallon kafa, ana hasashen za ta iya hada rukuni da Brazil da Spain da Jamus da Argentina.

Hodson ya ce "na fi damuwa akan filin da zamuyi wasanninmu, domin wasu filayan suna da wahalar buga kwallo a Brazil."

Ga jerIn kasashen da suke gaba gaba a kwallon kafa kamar yadda Fifa ta ayyana.

Argentina Belgium Brazil Colombia Germany Spain Switzerland Uruguay