''Dole ne Fulham ta sayi 'yan wasa''

Rene Meulensteen
Image caption Robin van Persie ya ce Meulensteen na daya daga cikin kwararrun kociyoyi a duniya

Sabon kociyan Fulham Rene Meulensteen ya ce dole ne kungiyar ta sayi 'yan wasa a watan Janairu domin samun damar tsira a Premier.

Ya ce, ''ya kamata kowa ya san cewa dole ne mu zuba kudi,''

''Muna bukatar mu duba yadda za mu karfafa kungiyar mu tabbatar Fulham ta ci gaba da zama a Premier.''

An nada Meulensteen a matsayin kociyan kungiyar ranar Lahadi bayan da aka kori Martin Jol bayan an yi galaba a kanta a wasanni biyar a jere inda take matsayin ta 18 a tebur.

A watan da ya wuce ne aka nada kociyan mai shekaru 49 wanda yayi aiki da Martin Jol bayan shekaru 12 yana aiki karkashin Sir Alex Ferguson a Man United.