Toure ne gwarzon dan kwallon Afrika na BBC na 2013

Image caption Yaya Toure

Yaya Toure ya zama gwarzon dan kwallon Afrika na BBC na 2013.

Dan kwallon Ivory Coast da Manchester City wanda sau hudu yana takara babu nasara, a bana ya doke Pierre-Emerick Aubameyang, Victor Moses, John Mikel Obi da kuma Jonathan don samun kyautar bana.

Dan shekaru 30 ya shaidawa BBC cewar "Abin da dadi saboda kamar sauran 'yan Afrika dole mutum ya ji dadin hakan. A matsayi na na dan Afrika naji dadin abun musamman saboda a baya a matakin kwallon kasa da kasa akwai karancin zaratan 'yan wasa ba kamar yanzu ba inda akwai Aubameyang, Pitroipa, Mikel, Moses, Kalou, da kuma Gervinho. A gaskiya a matsayi na na dan Afrika, na ji dadin hakan."

Kwararrun masana kwallon kafa a Afrika su 44 ne suka kebe sunayen ‘yan kwallonnan biyar, bisa la’akari da kwarewa da kwazo da kuma ladabi a cikin fili.

An kafa tarihi a yawan wadanda suka kada kuri’ar zaben gwarzon na bana.

Kuma masoya kwallon kafa sun zabi Toure a matsayin zakaran kwallon Afrika a wannan shekarar, musamman rawar da ya taka wajen bada kwallaye da kuma cin kwallayen.

Ko da yake a shekara ta 2013 bai lashe wata gasa ba, amma Toure ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin kasarsa da kungiyarsa sun haskaka.

Duk da cewar bai lashe gasar premier ta 2012 ba tare da Manchester City, Toure a kakar wasa ta bana ya kasance zakakurin dan wasan ga kulob din.

Image caption Yaya Toure

Ya zura kwallo a wasansu da Newcastle sai kuma ya kara ci a karawarsu da Hull.

Toure ya ci kwallaye hudu a bugun tazara cikin kwallaye bakwai da ya ciwa kulob dinsa.

A shekara ta 2013, kawo yanzu Toure ya ci kwallaye 12 wa kulob dinsa da kasarsa.

Ya taka muhumiyyar rawa wajen nasarar Ivory Coast wajen samun gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil a shekara ta 2014.

Sannan yana taka rawa wajen yaki da wariyar launin fata, bayan da aka nuna masa wariya a wasan zakarun Turai tsakaninsu da CSKA Moscow a watan Oktoba.

Bayan shafe shekaru biyar ana saka sunansa cikin wadanda za a iya baiwa kyautar gwarzon dan kwallon Afrika, Toure a bana ya zaman zakaran kwallon nahiyar Afrika na BBC.

Karin bayani