Mourinho: Sai mun gyara salon wasa

Jose Mourinyo
Image caption Kocin yana son ganin Chelsea ta lashe kofin Premier bana

Kocin Chelsea Jose Mourinyo ya ce sai sun sake salon wasa idan har suna son lashe kofin Premier bana.

Kocin ya sake dawo wa Chelsea a watan Yuni, bayan da ya lashe kofin Premier karo biyu a lokacin da ya horad da kungiyar a baya.

Duk da kungiyar tana matsayin ta biyu a teburin Premier, kocin ya ce sai sun zage dantse domin kaiwa gaci.

Rabon da Chelsea ta lashe kofin Premier tun shekarar 2010 a lokacin Carlo Ancelotti yana jagorantar kungiyar.

Bayan shekara guda kuma kungiyar ta lashe kofunan Turai na Champions da Europa League.