Premier : Crystal Palace da West Ham

Kociyan Crystal palace Tony Pulis
Image caption West Ham ce ta 15 yayin da Crystal Palace take matsayin ta karshe( 20) a teburin Premier

A yau ne za a kara tsakanin kungiyar Crystal Palace da West Ham a ci gaba da gasar Premier ta Ingila a wasa na mako na goma sha hudu.

Wannan shi ne wasan farko na gida da sabon kociyan Crystal Palace Tony Pulis zai jagoranta.

Dole ne kociyan ya yanke shawara ko zai yi sauyi a jerin 'yan wasansa da suka sha kashi a hannun Norwich 1-0 ranar Asabar da ta gabata.

A haduwar kungiyoyin sau hudu a baya West Ham ba ta yi galaba akan Crystal Palace ba a gidan 'yan Palace din Selhurst Park.

Sai dai ita kuma Crystal Palace ta yi nasara ne a gidan na ta sau biyu kawai a haduwarsu goma sha uku.

A haduwarsu ta Premier ta karshe a gidan Palace sun tashi 3-3 a watan Mayu na 1998.

Yanzu West Ham tana da maki 13 a wasanni 13 yayin da Crystal Palace ke da maki 7 a wasannin 13 na Premier.