Kompany zai buga wasan West Brom

Vincent Kompany
Image caption Dan wasan yana fama da jin raunuka a kakar bana

Kaftin din Manchester City Vincent Kompany zai dawo wasa a karawar da kungiyar za ta yi da West Brom ranar Laraba a gasar cin kofin Premier.

Dan wasan dan kasar Belgium mai tsaron baya, rabonsa da taka kwallo tun ranar 5 ga watan Oktoba a lokacin da suka lashe Everton da ci 3-1 a wasan da yaji rauni a cinyarsa.

Tun a satin da ya gabata ne dan wasan ya dawo atisaye, kuma yana cikin tawagar yan wasan City da za su bakunci filin wasa na The Hawthorns.

Kompany mai shekaru 27, tun a karawar da suka yi da Viktoria Plzen ranar 27 ga watan Satumba a gasar cin kofin zakarun Turai ya so ya buga wasa, amma likitoci suka ce bai gama murmure wa ba.