Nijeriya ta tsara ka'idojin ladan wasa

tambarin hukumar kwallon kafar Najeriya
Image caption Ko da yaushe 'yan wasa suna tada kayar baya a kan ladan wasa

Jami'an hukumar kwallon kafa ta Nijeriya na daf da fito da wasu ka'idojin ladan wasa da ake fatan za su magance ka-ce-na-ce a kan biyan 'yan wasa ladan buga wasa.

Hukumar na kokarin magance rigimar da ta faru a lokacin da kasar take kokarin buga gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya, wato Confederations Cup da kadan ya rage kasar ta fasa buga wasan.

'Yan wasan Najeriya sun yi yunkurin kin buga wasa, saboda an yanke musu kashi 50 cikin dari daga cikin kudin ladansu a wasannin shiga kofin duniya a watan Yuni a Kenya da Namibia.

Ministan wasanni Bolaji Abdullahi tare da kwamitin hukumar ne dai suka tsara ka'idojin da nufin fara amfani da su nan take ga 'yan wasan kwallon kafar kasar.