Wenger yayi watsi da masu hasashe

Alan shearer Alan Hensen
Image caption Wasu masu fashin baki har yanzu ba su da tabbacin Arsenal za ta lashe kofi

Arsene Wenger yayi watsi da hasashen da wasu masu fashin baki akan harkar wasanni ke yi cewa Arsenal ba za ta iya daukar kofin Premier bana ba.

Kungiyar tana matsayi na daya a teburi da tazarar maki hudu, a kokarin da take na lashe kofin bana, kuma rabonta da shi tun shekarar 2004.

Alan Shearer da Alan Hansen tsoffin 'yan wasa masu fashin baki a yanzu sun ce ba su da tabbacin cewa Arsenal za ta lashe kofin Premier a bana.

Wenger ya ce, "na dade da samun kwarewar fayyace abinda na ke yi da kuma yadda ya kamata na gudanar da shi. Ba sai wani ya gayamin ba."

Sai dai ya ce a shirye yake ya saurari masu shakkun kokarin kungiyar idan za su ba shi dalilan da zai amince da su.