An sayar da godiya fam miliyan 4

Godiya Dancing Rain
Image caption Ranar biyu ga watan Fabrairu ake saran godiya Dancing Rain za ta haihu

An sayar da godiyar tseren nan ta Ingila, mai suna Dancing Rain wadda ke da juna biyu da zakaran dokin tseren nan, Frankel akan fam miliyan 4 da dubu 200, kwatankwacin naira biliyan daya da miliyan 50.

An sayar wa John Ferguson mai bai wa Sheik Mohammed mai dokunan tsere na kungiyar Godolphin shawara godiyar.

Godiyar wadda aka yi wa ritaya daga shiga tsere ita ta yi nasara a gasar tseren Oaks ta 2011.

Shi ma Frankel wanda aka hada su barbara mallakar Yariman Saudiyya Khaled Abdullah an yi masa ritaya daga tsere a shekarar da ta wuce bayan ya yi nasara ta 14 a manyan gasanni 14.

Ana biyan fam dubu 125 yayi barbara sau daya, kuma zuwa karshen shekarassa ta farko a yada irin ana ganin an sami fam miliyan 15 da shi.

Wanda hakan ya ninka sau biyar yawan kudin gasar da aka samu da shi.