Nijeriya na neman wurin atisaye

kungiyar Super Eagles ta Najeriya
Image caption Najeriya na kokarin ganin ta taka rawar gani a Brazil

Jami'an hukumar kwallon kafa ta Nijeriya na shirye shiryen neman kasar da kungiyar kasar za ta yi atisaye, domin tunkarar gasar kofin Duniya na 2014.

Shugaban kwamitin tsare tsare na hukumar kwallon kafar kasar Chris Green ya ce sun dukufa wajen neman izinin atisaye a kasashen Colombia ko Argentina ko Amurka.

Ya kara da cewa wadannan kasashen suna da yanayi kusan daya da kasar Brazil, za kuma su karasa binciken gari da filin da zai fi dacewa da 'yan wasan.

Gasar ta badi da Najeriya za ta shiga ita ce karo na biyar da kasar ke halartar gasar cin kofin duniya, tun lokacin da ta halarci karonta na farko a 1994 a Amurka.

Hukumar kwallon kafar kasar ta tsai da duk wani shiri har sai an fid da jadawalin kasashen da za su fafata a gasar ta kofin duniya a ranar Juma'a