Caf: 'Yan Najeriya 4 a zaben bana

Yaya Toure
Image caption zakaran gwarzon kwallon Afrika na BBC a bana

'Yan kwallon Najeriya hudu na daga cikin guda 10 da hukumar kwallon Afrika ta fitar domin zaben gwarzon dan kwallon Afrika a bana.

'Yan wasan hudu sun hada da John Mikel Obi da mai tsaron raga Vincent Enyeama da Emmanuel Emenike da Ahmed Musa, dukkan su sun taimaka wa kasar samun gurbin gasar kofin duniya.

Mai rike da kambun na bara Yaya Toure dan kwallon Ivory Coast ya na daga cikin 'yan wasan da aka sake dauka don samun kyautar a bana, wanda tuni ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afrika na BBC a wannan satin.

Shi ma dan kwallon Masar Mohamed Aboutrika na daga cikin 'yan wasan da ake sa ran za su sami kyautar gwarzon dan wasan Afrikan amma ajin masu wasa a gida.

Mambobin hukumar kwallon Afrika da kwamitin 'yan jaridu ne dai suka rage yawan yan wasan zuwa 25 da kuma masu wasa a gida zuwa 12 da za a zabi gwarzon shekarar a cikinsu.