Mourinho: Man United na iya bazatta

jose mourinho
Image caption ''ko da ike dai abu ne mai wahala, amma idan Man United ce komai na iya kasancewa.''

Kociyan Chelsea Jose Mourinho bai fitar da tsammani kungiyar Manchester United za ta iya daukar kofin Premier bana ba.

Kociyan ya nuna cewa duk da tazarar maki 12 tsakaninta da Arsenal ta daya a tebur bai fitar da tsammanin kungiyar za ta farfado ba.

Amma kuma shi da kansa kociyan manchester United David Moyes ya ce, ''muna da doguwar tafiya a gabanmu.''

A jerin wasannin da aka yi na Premier ranar Laraban nan yayin da Chelsea ta ci Sunderland 4-3, Manchester United ta sha kashi a gidanta a hannun Everton tsohuwar kungiyar kociyanta.

Man United ta samu maki biyu ne kawai a wasanninta uku na baya bayan nan kuma ita ce ta tara a tebur da maki 22 a wasanni 14.

Kungiyar Chelsea ce ta biyu a wasanni goma sha hudu da maki talatin bambancin maki hudu tsakaninta da Arsenal.