Filayen kofin duniya ba za su kammalu ba

Sao Poulo Corinthians Venue
Image caption Daya daga cikin filin da ya sami koma baya a yayin aikin ginashi domin kofin duniya

Brazil ta sanar da cewa har yanzu ana aikace aikace a filayen da za a gudanar da gasar kofin duniya, kuma filayen ba za su kammalu ba kafin ranar da Fifa ta bukata a gama nan da ranar 31 ga watan Disamba.

Ministan wasanni na kasar Aldo Rebelo ya ce filayen wasanni shida da suka hada da na Sao Paulo da Curitiba da Porto Alegre da Cuiaba da Manaus da Natal sai a watan Janairu za a kammala su.

Matsalolin da suka kawo tafiyar hawainiya a ayyukan gina filayen sun hada da matsalolin magina da kuma zanga zanga kan kudin da za a kashe wajen gina filayen.

Fifa ta amince a cikin satinnan za ta kara wa'adin yarjejeniyar kwanankin da za a kammala aikin filayen.

Za a fara gasar cin kofin duniyar ranar 12 ga watan Yuni a filin wasa na Sao Paulo Arena Corinthians, filin da a satin da ya wuce ma'aikata biyu suka mutu bayan da wani karfen daga kayayyaki masu nauyi ya karye ya fado kansu.